
Likitocin da ke neman kwarewa sun shiga yajin aiki
Kungiyar likitoci masu neman kwarewar aiki a Najeriya sun shiga yajin aikin gargadi na kwanaki biyar.
Kungiyar ta ce ta É—auki wannan mataki ne sakamakon gwamnati ta gaza cika mata bukatunta da take nema duk da karin wa’adin kwanaki da ta bayar.
Yajin aikin da ake sa ran a janye zuwa ranar 16 ga watan Satumbar 2025 zai haifar da cikas ga ayyukan asibitoci da dama a Najeriya, musamman manyan asibitocin gwamnati da ke dogaro sosai da likitocin kasar.

