
Girgizar kasa ta afkawa arewacin Afghanistan
Mahukunta a kasar Afghanistan sun sanar da aukuwar wata girgizar kasa da ta yi sanadiyar mutuwar mutane 20 watanni kaɗan bayan aukuwar gargizar kasar da jefa kasar cikin Jimami.
Girgizar ƙasar da ke da ma’aunin 6.3 da ta auku cikin daren a kusa da garin Mazar-sharif tana zurfin kilomita 28.
Bayanan da ke fitowa daga kasar sun yi nuni da cewa mutane 534 suka jikkata, ya yin da aka kai gawarwaki kimanin 20 asibiti, da ke Samangan dake lardin a cewar mai magana da yawun ma’aikatar lafiya ta kasar.
Garin Mazar-sharif na daya daga manyan birane da ke arewacin Afghanistan.
Ma’aikatar tsaron ƙasar ta ce ta bada umarnin bude shigayen duba ababe hawa da suka haɗa garin na Mazar-sharif da kuma garin Kholm wanda hakan ya bada damar kai agaji ga mutanen da suke maƙale a wurare da dama.
Bankin Duniya ya ce a ƙiyasin da ya yi, girgizar kasa ta Afghanistan ta jawo hasarar kimanin Dala Miliyan 183 na gidaje da kuma sauran kayayyakin da suka lalace.

