Skip to content

Jihar Ebonyi ta amince da naira 90,000 a matsayin mafi karancin albashi

Gwamnatin jihar Ebonyi ta sanar da sabon mafi karancin albashin ma’aikata na naira 90,000,  inda ma’aikatan jihar suka samu karin naira 20,000 a kan mafi karancin albashin da aka amince da shi a baya. 

A cewar gwamnatin Ebonyi, karin zai fara aiki ne nan take. Wannan sabon matakin na zuwa ne bayan taron majalisar zartawar jihar da aka gudanar a ranar Laraba, a fadar gwamnati da ke Abakaliki.