Skip to content

Tinubu ya soke harajin kashi biyar na kira da data

Gwamnatin Najeriya ta soke harajin kashi biyar cikin 100 da aka sanya a kan kudin kiran waya da kuma intanet.

Hukumar Wayar da Kan Al’umma ta Kasa (NOA) ce ta sanar da hakan a wata takarda da ta fitar ranar Alhamis. Wannan matakin zai rage wa ’yan Najeriya matsin tattalin arziki, musamman ga masu amfani da waya da kuma intanet.

Wannan haraji na kashi biyar an fara kawo shi ne a lokacin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari.

Shugaban Hukumar Sadarwa ta Ƙasa (NCC), Aminu Maida ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar da wannan umarni ne na kudirin da aka gabatar na dokar haraji saboda da yawan kudin kira da data da ake ja wanda yan Najeriya ke korafi kansu

Ana dai ganin wannan sabon ci gaban zai kawo sauƙi ga mutane fiye miliyan 171 da ke amfani da wayoyin hannu a Najeriya, waɗanda da dama sun fuskanci ƙarin kuɗin kashi 50 a farashin kiran waya da data tun farkon shekarar nan.