
Gwamnatin Tinubu za ta magance Talauci
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya yi alƙawarin haɗa hannu da majami’u domin magance talauci, da samar da daidaito da kuma wanzar da zaman lafiya a cikin al’umma.
Tinubu ya ce haɗin gwiwar nada muhimmanci idan a ka yi la’akari da gudummawar da malaman addini suke bayar wa wajen gina alaka da sanya yarda a tsakanin al’umma.
Shugaban da ya sami wakilcin sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume a wajen taron Bishop-Bishop na mabiya darikar Katolika a Ikot Ekpene, ya bukaci malaman su ci gaba da nuna koyarwar addinin na haɗin kai da kuma ƙyamatar rikici da ke tarwatsa al’umma.
A cewarsa, gwamnatinsa ta shigo ne da manufar samar da sauyi da karfafa Dimokuraɗiyya ta yadda kowane ɗan ƙasa zai amfana.

