Skip to content

Saudiyya ta saki ‘Yan Najeriya da aka zarga da safarar kwayoyi.

Mahukunta a ƙasar Saudiyya sun saki mahajjatan Najeriya uku da tsare a birnin Jidda sakamakon zarginsu da safarar kwayoyi.

Ƴan Najeriya ukun da aka saki bayan kwashe sati huɗu a tsare sun hada da Maryam Hussain Abdullahi da Abdullahi Bahijja Aminu da kuma Abdulhamid Saddiq.

Da yake jawabi a wajen taron manema labarai, mai magana da yawun hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, Femi Babafemi ya ce sakin na su ya zo ne bayan jajircewar shugaban hukumar ta NDLEA Burgediya Janar Mohammed Buba Marwa mai ritaya, da shugabacin hukumar dakile yaɗuwar kayan maye a kasar Saudiyya da kuma goyon bayan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Idan za’a iya tunawa, ma’aikata a tashar jirgin sama ta Malam Aminu Kano sun gano kwayoyi a cikin wasu jakunkuna da ke dauke da sunayen wadanda aka saka.

Marwa ya yaba da kokarin dukkan masu ruwa da tsaki wajen tabbatar da sakin Mahajjatan bayan gano gaskiyarsu.