Skip to content

Tiwa Sawage- An tozarta ni a tsohuwar soyayyata

Fittaciyar mawakiyar nan ta Najeriya, Tiwa Savage ta ce ba a girmamata ba a cikin soyayyar da ta yi a baya. Mawakiyar da ta bayyana hakan a wani shiri na Joe Budden, ta ce ta boye wancar alakar ce sakamakon saurayin; wanda shi ma sanannen dan masana’antarsu ne ya bukaci su boye wa duniya soyayyarsu.

Ta ce tsohon saurayin nata kan yi abubuwan da ya ga dama ga sauran mata, duk da cewa ya san suna soyayya, amma kuma bai mutunta ba. Ta kara da cewa, yana yin hakan ne inda a cewarsa, mutane ba za su gane alakarsa da ita ba.

A lokacin da take bayyana takaicinta, Tiwa ta ki fadin sunan tsohon saurayin, sai dai mutane da zargin cewa mawaki, Wizkid ne.