
Ana fargabar rasa rayuka bayan Nutsewar Kwale-Kwale a Sokoto
Rohatonni sun yi nuni da cewa, an sake samun nutsewar kwale-kwale a jihar Sokoto, inda ake fargabar rasa rayuka.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, kwale-kwale na ɗauke ne da mata da ke gudun ceton rai daga hare-haren yan bindiga, wanda ya maƙale da misalin karfe 7:30 na daren ranar Alhamis. Mahukunta na ci gaba da bincike domin gano wadanda hatsarin ya rutsa da su.

