
An yankewa wani soja hukuncin rataya a Bauchi
Wata kotun sojoji a jihar Filato ta yanke wa sojan Nijeriya hukuncin rataya bayan kama shi da laifin kisan wani matashi.
Kotun ta yanke wa Lukman Musa hukunci bayan ta same shi da laifin kisa, haɗin baki da mallakar harsashi ba bisa ƙa’ida ba, ƙarƙashin jagorancin Birgediya Janar Liafis Bello.
A shari’ar, kotun ta ce, Musa da abokin sa Oba sun jawo Isa cikin gidan sa da sunan taimaka masa, sai suka buge shi sannan suka shake shi.
Domin boye laifin sa, Musa ya saka gawar mai Keke Napep a cikin jaka, ya yar a tsakanin ƙauyen Shira da Yala, inda daga baya aka sayar da Keken.
Kotun ta kuma kama Musa da mallakar harsai guda 34 na 7.62mm ba tare da izini ba, lamarin da ya ƙara nauyin tuhume-tuhumen sa.
An yanke masa hukuncin kisa bisa dokar ‘Penal Code’ sashe na 220, yayin da aka kuma yanke masa shekara biyu a kurkuku bisa mallakar harsashi.
Haka kuma kotun ta kori Musa daga aikin soja tare da bayyana shi a matsayin wanda ya saba wa tsarin aiki da na doka.

