
An yi gwajin kwaya kan matukin jirgin Air Peace
Wani bincike da hukumar binciken sufuri ta Najeriya (NSIB) ta fitar kan matukin jirgin kamfanin Air Peace da mai taimaka masa ya yi nuni da cewa, suna ta’amulli da miyagun kwayoyi. Binciken dai ya biyo bayan wata matsala da aka samu yayin da wani jirgi yake sauka a filin jirgin Fatakwal a watan Julin wannan shekarar.
Binciken ya bankado cewa an samu alamun shan giya a jikin wasu daga cikin ma’aikatan jirgin na ranar mai dauke da fasinjoji 103, yayin da guda daga cikinsu kuma aka gano wata kwaya mai alaka da tabar wiwi a jikinsa. Hukumar NSIB ta ce ta na duba ta yadda wannan matsala ka iya shafar ayyukan da ma’aikatan jirgin za su gudanar da kuma lafiyar fasinjoji, kamar yadda jaridar DailyTrust ta ruwaito.

