Da yawa daga cikin manoman da kuma kungiyoyin su a ganawar su da jaridar Daily Trust,na ganin gwamnatin tarayya ce ke da laifi game da musabbabin faɗuwar farashin kayyakin abincin ta hanyar bada dama a shigo da abinci cikin kasar nan, abin da ya yi sanadiyar karyewar farashin abincin. Sai kuma ƙaramin ministan goma da
Hukumar kula da kamfanoni da Kare masu amfani da kayayyaki ta Najeriya ta gargadi al’umma game da abinci masu haɗari da ke yawo a kasuwanni, waɗanda ke jefa rayukan miliyoyin ‘yan ƙasa cikin haɗari a kasar nan Hukumar ta fitar da wannan gargadi ne yayin wani taron wayar da kai na yini guda da aka
Rahotanni sun nuna an sami hatsaniya a tsakanin masu gudanar da zanga-zanga da kuma jami’an tsaro a Abuja. Masu zanga-zangar karkashin jagorancin Omoyele Sowore na naiman gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinuu ta sani Nnamdi Kanu jagoran masu naiman Kafa kasar Biafra. Tun bayan fara zanga-zangar a Litinin din, mahukunta a babban birnin tarayya Abuja
Ƙungiyar likitoci masu neman kwarewa ta Najeriya, ta nuna damuwarta a kan ƙarancin likitoci, inda ta ce kididdiga ya nuna cewa kowane likita guda ɗaya na duba marasa lafiya fiye da 19,000, wanda hakan kuma ya saɓa da tsarin aikin a duniya A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, albarkacin cikan ƙasar shekaru 65 da
Cibiyar kula da hakan ma’adanai ta ƙasa ta koka bisa yadda ake samun yawan hatsarurka a wajajen hakan ma’adanai a Najeriya. Hakan ya biyo bayan ruftawar wani wajen hakan ma’adanai a ƙauyen Jagaba da ke ƙaramar hukumar Maru da ke cikin jiha Zamfara, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane goma sha uku 13 da kuma
Gwamnatin Jihar Kogi ta bayyana alhininta game da rasuwar aƙalla mutum 26 waɗanda hatsarin jirgin ruwa ya rutsa da su. Mutanen sun fito ne daga Ƙaramar Hukumar Ibaji, kuma suna kan hanyarsu ta zuwa kasuwar Ilushi a Jihar Edo. Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar, Kingsley Fanwo ne, ya bayyana hakan a Lokoja a ranar Laraba.
Rohatonni sun yi nuni da cewa, an sake samun nutsewar kwale-kwale a jihar Sokoto, inda ake fargabar rasa rayuka. Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, kwale-kwale na ɗauke ne da mata da ke gudun ceton rai daga hare-haren yan bindiga, wanda ya maƙale da misalin karfe 7:30 na daren ranar Alhamis. Mahukunta na ci gaba
Wata kotun sojoji a jihar Filato ta yanke wa sojan Nijeriya hukuncin rataya bayan kama shi da laifin kisan wani matashi. Kotun ta yanke wa Lukman Musa hukunci bayan ta same shi da laifin kisa, haɗin baki da mallakar harsashi ba bisa ƙa’ida ba, ƙarƙashin jagorancin Birgediya Janar Liafis Bello. A shari’ar, kotun ta ce,
Fittaciyar mawakiyar nan ta Najeriya, Tiwa Savage ta ce ba a girmamata ba a cikin soyayyar da ta yi a baya. Mawakiyar da ta bayyana hakan a wani shiri na Joe Budden, ta ce ta boye wancar alakar ce sakamakon saurayin; wanda shi ma sanannen dan masana’antarsu ne ya bukaci su boye wa duniya soyayyarsu.