Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta mayar da tsarin koyar da tarihi a manhajar makarantun ƙasar, wanda hakan zai samar da haɗin kai da kuma sanar da asalin daga inda kowace al’umma ta fito. A karon farko cikin shekaru goma da suka gabata ɗalibai tun daga matakin makarantar firamare da ƙaramar sakandiri, da kuma aji ɗaya na
Shirin Matasa da Rayuwa ya duba irin kalubalen da masu fasahar kirkire-kirkire ke fuskanta a Najeriya.
Noma na duƙe tsohon ciniki kowa ya zauna duniya kai ya tarar, wannan shi ne kirarin da ake wa noma tun fil azal, kuma kamar yadda aka sani ne an san mutanen yankin arewacin kasar nan da noma wanda suka gada tun kaka da kakanni, da ke ba su damar samar da isasshen abinci ga
Mahukunta a ƙasar Saudiyya sun saki mahajjatan Najeriya uku da tsare a birnin Jidda sakamakon zarginsu da safarar kwayoyi. Ƴan Najeriya ukun da aka saki bayan kwashe sati huɗu a tsare sun hada da Maryam Hussain Abdullahi da Abdullahi Bahijja Aminu da kuma Abdulhamid Saddiq. Da yake jawabi a wajen taron manema labarai, mai magana
Wani mummunan haɗarin mota da ya auku ajihar Zamfara na arewacin Najeriya ya yi sanadiyar mutuwar mutane 19, cikin fasinjoji 40 da suke cikin motar. Lamarin ya auku ne a ƙauyen Gwalli da ke yankin karamar hukumar Gimi, kuma motar na ɗauke ne da masu kai amarya kimanin mutum 40 inda motar ta faɗa cikin
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya yi alƙawarin haɗa hannu da majami’u domin magance talauci, da samar da daidaito da kuma wanzar da zaman lafiya a cikin al’umma. Tinubu ya ce haɗin gwiwar nada muhimmanci idan a ka yi la’akari da gudummawar da malaman addini suke bayar wa wajen gina alaka da sanya yarda a
Runduna ‘yan sandan jihar Nassarawa ta cafke wata matashiya bisa samu ta da laifin jefar da jaririyarta a garin Akwangan jihar Nassarawa. Kakakin rundunan ‘yan sandar da ke jihar, SP Rahaman Nansel ya sanar da hakan ga manema labarai a garin Lafiya, ya ce tuni rundunar ‘yan sandar ta gano tare da cafke matar bayan
Kungiyar likitoci masu neman kwarewar aiki a Najeriya sun shiga yajin aikin gargadi na kwanaki biyar. Kungiyar ta ce ta ɗauki wannan mataki ne sakamakon gwamnati ta gaza cika mata bukatunta da take nema duk da karin wa’adin kwanaki da ta bayar. Yajin aikin da ake sa ran a janye zuwa ranar 16 ga watan
Gwamnatin Najeriya ta soke harajin kashi biyar cikin 100 da aka sanya a kan kudin kiran waya da kuma intanet. Hukumar Wayar da Kan Al’umma ta Kasa (NOA) ce ta sanar da hakan a wata takarda da ta fitar ranar Alhamis. Wannan matakin zai rage wa ’yan Najeriya matsin tattalin arziki, musamman ga masu amfani