
Fadada hanyoyin samun lantarki a Najeriya
Gwamnatin Najeriya na duba yiwuwar bai wa jahohi 36 da ke faɗin ƙasar damar kafa tashoshin lantarki a jahohinsu domin samar da shi da kuma rarraba shi ga jama’a.
Gwamnatin ta ce wannan hanyar ce ta magance ƙarancin lantarki. Ministan lantarkin kasar, Adebayo Adelabu ya fadi hakan a Legas a wajen wani taron ƙoli game da hasken lantarki.
Gwamnatin ta ce duk yunkurin da aka yi a baya na samar da isasshen lantarki amma kwalliya bata biya kuɗin sabulu ba, hakan ya sanya gwamnatin tarayya duba yiwuwar bai wa jahohi 36 wannan damar.
Ministan ya ƙara da cewa halin da ake ciki na samar da lantarkin bai daya ba zai yiwu ba a kasar, ya ce adon haka bai wa jahohi dama su samar da lantarkin ga jama’ar su shi ne mafita kawai.
Ya ƙara da cewa idan aka bai wa jahohi wannan damar zai sanya gasa wajen sayar da lantarkin ga al’umma, da kuma samun ingartuwar lantarki da kuma karfafa guwiwar ɓangarori masu zaman kansu domin su shiga a dama da su wajen harkokin lantarkin yadda ya kamata.

