Skip to content

Gomman mutane sun mutu a Kogi

Gwamnatin Jihar Kogi ta bayyana alhininta game da rasuwar aƙalla mutum 26 waɗanda hatsarin jirgin ruwa ya rutsa da su.

Mutanen sun fito ne daga Ƙaramar Hukumar Ibaji, kuma suna kan hanyarsu ta zuwa kasuwar Ilushi a Jihar Edo.

Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar, Kingsley Fanwo ne, ya bayyana hakan a Lokoja a ranar Laraba.

Ya ce wannan lamari babban rashi ne, kuma gwamnatin jihar na miƙa ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasu da al’ummar Ibaji gaba ɗaya.

Gwamna Ahmed Usman Ododo, ya aike ta’aziyyarsa, inda ya ce gwamnatin jihar na tare da al’ummar Ibaji a wannan lokaci na baƙin ciki.

Ya bai wa Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar da sauran hukumomi, umarnin su bai wa waɗanda abin ya shafa tallafi.

Gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatin za ta ci gaba da aiki tare da Hukumomin Tarayya domin ƙara tsaro a harkar sufuri ta ruwa, don guje wa faruwar irin wannan iftila’i a nan gaba.

Haka kuma ya shawarci al’umma da su guji loda mutane da yawa a cikin jirgi, kuma suke amfani da rigar ruwa da sauran hanyoyin kariya idan suna tafiya ta ruwa.