Skip to content

Gwamnatin Najeriya ta fitar da sabon tsari ga manoma

Gwamnatin Najeriya ta fitar samar da wani tsarin a harkar aikin gona da zai kawo karshen yunwa da kuma samar da wadataccen abinci, da kuma rage irin asarar da manoma ke samu a lokacin girbi wanda hasarar da ake yi ta kai ta dallar miliyan dubu goma a duk shekara.

Ministan aikin gona da samar da wadataccen abinci, Sanata Abubakar Kyari da kuma ƙaramin ministan aikin gona ne suka tabbatar da hakan a wata sanarwar haɗin gwiwa da suka sanyawa hannu a ranar Alhamis ɗin nan.

Minista kyari ya ce har kwanan gobe noma ne kashin bayan cigaban tattalin arzikin ƙasar nan, haka nan kuma a cewar sa harkar noma shi ke hanya ɗaya tillo da ke samar da ayyukan yi, da kuma sanar da cewa harkar noma na samar da kaso mai dama wajen habaka tattalin arzikin ƙasa.

Kyari ya ce tuni gwamnati ta samar da wasu tsare-tsare masu ingancin da za su inganta bangaren aikin goma.