Skip to content

Hukumomi na gargadi a Najeriya kan wasu na’ukan abinci da suke a kasuwanni

Hukumar kula da kamfanoni da Kare masu amfani da kayayyaki ta Najeriya ta gargadi al’umma game da abinci masu haɗari da ke yawo a kasuwanni, waɗanda ke jefa rayukan miliyoyin ‘yan ƙasa cikin haɗari a kasar nan

Hukumar ta fitar da wannan gargadi ne yayin wani taron wayar da kai na yini guda da aka gudanar a Jos, babban birnin Jihar Filato.

Da yake jawabi a wurin taron, Mataimakin Shugaban Hukumar, Olatunji Bello, ya ce suke da alhakin kare da kuma inganta muradu da walwalar masu amfani da kayayaki tare da tabbatar da adalci a tsakanin masana’antu.

Mataimakin Shugaban, daya sami wakilcin Daraktar Sashen Kula da Inganci da Ci gaba, Dakta Nkechi Mba, ta ce abinci ba kawai abu ne na ciyarwa ko kayan kasuwanci ba, wani ɓangare ne na amma haƙƙin ɗan Adam.

A nata jawabin, Mataimakiyar Babbar Ma’aikaciyar Dakin Gwaje-gwaje ta Hukumar NAFDAC, Evelyn Garba Pofi, ta ce: “Amfani da sinadarin calcium carbide yana haifar da matsaloli masu tsanani ga lafiyar masu amfani da kaya . Daga cikin waɗannan matsalolin akwai cutar daji ta koda da hanta, cutar daji ta fata, matsalar baki, ƙaiƙayi, da sauran matsalolin lafiya da dama.”