
Karancin likitoci a Najeriya
Ƙungiyar likitoci masu neman kwarewa ta Najeriya, ta nuna damuwarta a kan ƙarancin likitoci, inda ta ce kididdiga ya nuna cewa kowane likita guda ɗaya na duba marasa lafiya fiye da 19,000, wanda hakan kuma ya saɓa da tsarin aikin a duniya
A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, albarkacin cikan ƙasar shekaru 65 da samun ƴanci, ta ce ƙarancin likitcin da ake fuskanta ya nuna koma bayan da ake dashi a tsarin kiwon lafiya.
Kungiyar ta ce daga ranar 1 ga watan Oktobar 2025, likitoci masu neman ƙwarewa ba za su ci-gaba da amsa kiran daya wuce awa 24 ba.
Sanarwar da ta samu sa hannun shugaban ƙungiyar Dr. Mohammad Suleiman da sakatarenta Dr Shu’aibu Ibrahim da kuma sakataren wayar da kan al’umma Dr. Abdulmajid Ibrahim, ta ce Najeriya na ci gaba da fuskantar karancin likitocin wanda kuma na da alaƙa da yadda likitocin ke tafiya kasashen ketare domin neman aiki mai gwaɓi.
Ƙungiyar ta yi kira ga ma’aikatar lafiya ta da aiwatar da tsare-tsaren da aka samar domin ragewa likitoci ayyukansu tare da samar da wasu dokoki da zasu takaita yadda ake kiran likitoci akai-akai domin samun lafiyar likitocin da kuma Marasa Lafiya.

