
Mahimmancin dawo da darasin tarihi a makarantun Najeriya
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta mayar da tsarin koyar da tarihi a manhajar makarantun ƙasar, wanda hakan zai samar da haɗin kai da kuma sanar da asalin daga inda kowace al’umma ta fito.
A karon farko cikin shekaru goma da suka gabata ɗalibai tun daga matakin makarantar firamare da ƙaramar sakandiri, da kuma aji ɗaya na babbar sakandiri har zuwa aji uku na babban sakandiri za a riƙa koyar da su ilimi tarihi da illimin zamantakewa da sauran fannoni daban daban.
A cewar ma’aikatar ilimi wannan tsarin wani tagomashi ne kuma wata kyauta ce ta musamman ga ɗaliban ƙasar nan, yadda za su san asalin su daga ina suke kuma ina suka dosa wanda hakan zai kawo haɗin kai a ƙasar nan.
Tuni dai a cewar sanarwar ma’aikatar ilimin ta fitar da sabon tsarin jaddawalin karatun a cikin manhajar karatun, kana ta tsara yadda za a samar da malamai da kayyakin koyo da kuma sanya ido domin cigaban shirin.

