Skip to content

Matsalar takin zamani ga manoma

Noma na duƙe tsohon ciniki kowa ya zauna duniya kai ya tarar, wannan shi ne kirarin da ake wa noma tun fil azal, kuma kamar yadda aka sani ne an san mutanen yankin arewacin kasar nan da noma wanda suka gada tun kaka da kakanni, da ke ba su damar samar da isasshen abinci ga ƙasar nan. Sai dai wani lamarin da ke ci wa manoman tuwo a kwarya shi ne matsalar rashin takin zamanin mai sauƙi da kuma wadatar ce, wasu daga cikin manoman da kafar Hausa view ta zanta da su sun nuna rashin jin daɗin su bisa yadda gwamnati ke jen ƙafa wajen samar da takin kan lokaci kamar yadda ake yi can baya.

Malam Haruna Abdullahi da ya kasance tsohon ma’aikaci ne a wata tsohuwar hukumar da gwamnati ta kafa a wancan lokaci wadda kuma ke samar da kayayyakin aikin noma cikin sauƙi wadda ake kira da Pascom, wanda a halin yanzu ya rungumi aikin noma ya koka ne kan yadda harkar samar da taki a makare ba kamar da ba da hukumar ta Pascom take bayar wa ba.

A ƙasashen da suka ci gaba irin su Chaina, suna bai wa aikin gona mahimmancin gaskiya wanda hakan ya sanya suka fi kowace kasa samar da abinci ga al’ummar ƙasar su da ma sauran ƙasashen duniya, hakan ya sanya idan dai har ana son cimma burin wadata ƙasa da abinci to dole ne ayi koyi da irin su Chaina