
Mutane 19 sun mutu a Zamfara sakamakon hadarin mota
Wani mummunan haɗarin mota da ya auku ajihar Zamfara na arewacin Najeriya ya yi sanadiyar mutuwar mutane 19, cikin fasinjoji 40 da suke cikin motar.
Lamarin ya auku ne a ƙauyen Gwalli da ke yankin karamar hukumar Gimi, kuma motar na ɗauke ne da masu kai amarya kimanin mutum 40 inda motar ta faɗa cikin kogi lokacin da suke ƙoƙarin haye kogin, ta kan wata gadar da aka yi ta na wucin gadi.
Sai dai kuma amaryar da direban da wasu fasinjojin 21 suna daga cikin waɗanda suka tsira da rayuwarsu, sai a dai a lokacin haɗa wannan rahoto an gano gawarwaki 17.
Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Zamfara, DSP Yazid Abubakar ya nuna jimamin shi kan aukuwar lamarin, sai dai ya danganta aukuwar haɗarin ga sanya mutanen da suka wuce ƙima a cikin motar.
DSP Yazid Abubakar sai ya yi kira ga direbobi da su guji laftawa mota fasinjoji da kuma kayan da suka wace kima.

