Skip to content

Najeriya na shirin karbar sabbin masu zuba jari

Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Harkokin Kuɗi, Sanata Sani Musa ya bayyana cewa Najeriya ta shirya tsaf domin karɓar masu zuba jari bayan sauye-sauyen da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aiwatar a fannin tattalin arziki.

Sanatan ya bayyana haka ne yayin zaman tattaunawar kungiyar Tarayyar Turai EU da wasu kasashen Afirka” mai taken”Rage Barazanar Zuba Jari da Tura Kuɗaɗe, da Hanyar Cike Gibin Zuba Jari a Afirka.

Ya yi kira ga manyan ƙungiyoyin kasashen waje da su mayar da hankali wajen zuba jari kai tsaye a cikin gida, maimakon dogaro da tsare-tsaren da ba sa amfani kai tsaye ga ‘yan ƙasa.

Sanata ya kara da cewa, Najeriya wata ƙasa ce da sauran ƙasashen Afrika za su iya ɗauka tamkar abin koyi nan gaba, domin mu ne ƙasa mafi yawan jama’a, kuma yawan matasanmu masu ƙarfi da aiki ya fi yawa.

Ya kara da cewa Afrika na da kashi 17 cikin 100 na yawan al’ummar duniya, amma abin takaici ƙasa da kaso shida ne yake shigowa Afrika a matsayin zuba jari, ya kuma yi kira ga abokan hulɗa su cigaba da saka hannun jarin su a ciki.