
Najeriya ta fara fitar da bashi na naira miliyan 10 marar ruwa karkashin asusun tallafawa manyan makarantu.
Shirin an samar da shi ne domin bunkasa kwazon aikin ma’aikatan jami’o’I da kwaleji-kwalejin ilimi a kasar nan.
A wajen taron kaddamar da fara bayar da bashin da aka gudanar da jami’ar kimiyya ta tarayya dake Akure, ministan ilimi Tunji Alausa ya bayyana Shirin a matsayin wata nasara ta shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu wanda ya fifita tallafawa rayuwar Al’umma da kuma ilimi.
Alausa ya bayyana cewa, shirin TISSF yana bai wa ma’aikata damar karɓar lamuni marar riba har zuwa Naira miliyan 10, amma ba zai wuce kashi ɗaya bisa uku na albashin shekara-shekara na mai nema ba. Lamunin zai taimaka wajen gina gida, kula da lafiya, samun abin hawa, ko kuma fara karamin kasuwanci.
Ya ce ma’aikata fiye da 9,000 daga jami’o’i da kwalejoji 219 na tarayya da jihohi sun fara karɓar takardun amincewa da kuma biyan kuɗi, yayin da fiye da mutum 400 aka riga aka biya su.
Ya bukaci masu amfana da su biya lamunin cikin lokaci, domin shirin yana dogaro da dawowar kuɗi don ya ci gaba da amfanar da wasu a gaba.
Ministan ya ƙara da cewa an kafa tsarin bincike da lura a duk bayan watanni uku domin tabbatar da gaskiya, da nagarta, da kuma dorewar shirin.
