
Rashin jituwa kan farashin abinci a Najeriya
Da yawa daga cikin manoman da kuma kungiyoyin su a ganawar su da jaridar Daily Trust,na ganin gwamnatin tarayya ce ke da laifi game da musabbabin faɗuwar farashin kayyakin abincin ta hanyar bada dama a shigo da abinci cikin kasar nan, abin da ya yi sanadiyar karyewar farashin abincin.
Sai kuma ƙaramin ministan goma da wadata ƙasa da abinci, Aliyu Sabi Abdullahi ya ce sam ba haka bane, amma kuma irin ingantattun tsare-tsare ne da gwamnati ta fito da su domin samar da abinci ne ya fara aiki.
To sai dai manoman na kokawa game da tsadan kayayyakin aikin gona wanda a cewar su haka ba zai haifar da ɗa mai ido ba a bangaren aikin gona nan.
Idan za a iya tunawa dai a cikin watan Satumba 2024 gwamnati ta shelanta cire kuɗin haraji na kayyakin masarufi da suka haɗa da masara da shinkafa da kuma Alkama na tsawon kwanaki 150.

