
Rikicin PDP: Kwamitin Amintattu ya mara wa Damagum baya
Kwamitin amintattu na jam’iyyar adawa ta PDP ya kafa kwamitin mutane shida domin sasanta rikicin da ke tsakanin ɓangarorin jam’iyyar, yayin da ake samun rashin jituwa a game da shugabancin jam’iyyar na ƙasa.
Shugaban kwamitin wanda tsohon Shugaban Majalisar Dattawa ne Adolphus Wabara, ya tabbatar da cewa Ambasada Umar Iliya Damagum shi ne sahihin mukaddashin shugaban kwamitin zartarwa na ƙasa.
Wannan mataki ya zo ne kwana biyu bayan wani ɓangare na kwamitin aiki da cikawa da ke goyon bayan Alhaji Abdulrahman Muhammed tare da Sakataren Jam’iyya, Sanata Samuel Anyanwu, suka mamaye sakatariyar jam’iyar ta PDP a Abuja.
A cikin wata sanarwar bayan taro da kwamitin amintattu ya fitar a Abuja a ranar Laraba, kwamitin ya bayyana kansa a matsayin rubin jam’iyyar, yana mai cewa ba zai ɗauki ɓangare ba sai dai ya tsaya tsayin daka wajen kare mutuncin jam’iyyar da ƙarfafa tattaunawa.
Kwamitin amintattun ɗin ya ce an kafa Kwamitin Sulhu ne domin dawo da haɗin kai yayin da jam’iyyar ke shirin gudanar da babban taronta a Ibadan dake Jihar Oyo, a ranar 15–16 ga Nuwamba.

