Skip to content

Sabbin tsare-tsaren inshorar lafiya ga ‘yan Najeriya

Hukumar Inshorar lafiya ta Najeriya ta ce ta samar da sabbin tsare-tsaren kula da lafiyar da za su saukaka wa marasa lafiya, musamman mata da masu ƙananan karfi.

Shugaban hukumar a jihar Kaduna, Aminu Tanimu ne ya bayyana haka a wajen taron ƙarawa juna sani da aka gudanar a Kaduna.

Tanimu ya ce daga shekarar 2024 zuwa yanzu, an gabatar da sauye-sauye da suka hada da sabbin farashin magunguna da shiri na musamman ga marasa galihu da ba sa iya biyan kuɗaɗen tiyata na haihuwa da kuma ma su lalurar yoyon fitsari, wanda gwamnati ta ɗauki nauyin yi masu aiki ƙyauta.

Shugaban ya ƙara da cewa, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya umurci dukkan hukumomi da kuma ma’aikatun gwamnati su aiwatar da shirin inshorar lafiya bisa ga dokar hukumar ta shekarar 2022 da aka yi wa ƙwaskwarima.