
Sarki Sunusi ya magantu kan cire tallafin mai
Sarkin Kano na 16 kuma tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Muhammadu Sanusi II, ya nuna shakku a kan dalilin ci gaba da karɓar bashi bayan cire tallafin man fetur da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi.
Da yake jawabi a Abuja yayin taron Oxford Global Think Tank Leadership Conference da ƙaddamar da wani littafi, sarkin ya ce cire tallafin man fetur ya ƙara wa gwamnati samun kuɗin shiga.
Sanusi ya yaba wa gwamnatin Tinubu bisa cire tallafin mai da kuma daidaita farashin musayar kuɗi, yana cewa waɗannan matakan “masu tsauri ne amma wajibi ne a ɗauka.”
Sai dai ya gargadi cewa waɗannan gyare-gyaren za su gaza cimma nasara idan har ba a haɗa su da tsauraran dokokin kashe kudade da gaskiya wajen amfani da su ba.

