Skip to content

Wata mata ta yar da jaririya a Nasarawa

Runduna ‘yan sandan jihar Nassarawa ta cafke wata matashiya bisa samu ta da laifin jefar da jaririyarta a garin Akwangan jihar Nassarawa.

Kakakin rundunan ‘yan sandar da ke jihar, SP Rahaman Nansel ya sanar da hakan ga manema labarai a garin Lafiya, ya ce tuni rundunar ‘yan sandar ta gano tare da cafke matar bayan ta gudanar da binciken ƙwaƙwaf kan aukuwar lamarin.

A cewar SP Nansel, tuni kwamishina ‘yan sandar jihar ya bada umarni mika wa sashin binciken manyan laifuka lamarin domin gudanar da binciken ƙwaƙaf inda daga bisani a miƙa ta zuwa kotu.

An dai tsinci jaririyar ne a kusa da sananniyar makarantar nan wato AA koto da ke yankin Akwanga, nannaɗe ciki tsumma.

Shaidun gani da Ido sun fadawa manema labarai cewar matar data jefar da jaririyar Ɗaliba ce dake shekarar ƙarshe a tsangayar Ilimi ta makarantar horon malamai wato NCE dake Akwanga.