
‘Yan Najeriya miliyan 24 na fama da makanta
Jami’ar Tarayyar ta David Umahi da ke Uburu a jihar Ebonyi ta ce a kalla ƴan Najeriya miliyan 24 ne a yanzu ke fama da lalurar makanta a kasar.
Shugaban jami’ar, Farfesa Jesse Uneke ne ya bayyana haka lokacin ganawarsa da manema labarai a kan ayyukan cibiyar nazari da kula da lafiyar ido a garin Uburu da ke karamar hukumar Ohaozora.
Uneke ya ce binciken da aka gudanar a kan lalurar gani a kasar ya nuna cewa, a kalla kaso 4.2 na ƴan Najeriya da suka haura shekaru 40 ke fama da lalurar rashin gani.
A cewarsa, “Kaso 84 na masu lalurar makanta a Najeriya na faruwa ne saboda rashin ɗaukan matakan kariya, kuma akwai bukatar a rika ganin likita akai-akai da wayar da kan al’umma da kuma samar da magunguna”
Farfesan ya kara da cewa, ƙarancin kayan kula da lafiyar idanu a kasashe irin Najeriya na ɗaya daga cikin abin da ke kara ta’azzara matsalar rashin gani musamman a yankunan karkara.

