Skip to content

‘Yan sanda na neman Sowore ruwa a jallo

Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Legas ta bayyana cewa tana neman mai fafutukar kare haƙƙin ɗan adam kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Omoyele Sowore ruwa a jallo, bisa zargin tayar da hankalin jama’a.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Legas, Olorundare Jimoh, ya bayyana cewa ya taɓa gargadin Sowore da kada ya sake ya shirya zanga-zangar nuna adawa da kuma rushe gine-ginen da ake yi a yankin Oworonshoki, wanda gwamnatin jihar ta ce tana yin sa ne a cikin shirin na sabunta birni.

Duk da wannan gargadi, mambobin ƙungiyar Sowore sun fito a yau Litinin inda suka gudanar da zanga-zangar lumana, suna nuna rashin jin daɗi game da rushewar gidaje.

Sai dai ‘yan sanda masu yaƙi da tarzoma tare da jami’an sa kai na jihar sun fesa hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa masu zanga-zangar.

Haka zalika Rahotanni sun nuna cewa Sowore bai halarci zanga-zangar ba, amma duk da haka, Kwamishinan ‘Yan Sanda ya bayyana shi a matsayin wanda ake nema, bisa zargin shirya tada tarzoma