Skip to content

‘Yan sanda sun tarwatsa masu boren neman sakin Nnamdi Kanu

Rahotanni sun nuna an sami hatsaniya a tsakanin masu gudanar da zanga-zanga da kuma jami’an tsaro a Abuja.

Masu zanga-zangar karkashin jagorancin Omoyele Sowore na naiman gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinuu ta sani Nnamdi Kanu jagoran masu naiman Kafa kasar Biafra.

Tun bayan fara zanga-zangar a Litinin din, mahukunta a babban birnin tarayya Abuja suka kara tsaurara tsaro a yankunan Bwari da Zuba da kuma Nyanya kamar yadda jaridar Daily trust ta ruwaito.

Lamarin ya haifar da cunkuson ababen hawa domin dakile zanga-zangar.

Nnamdi Kanu jagoran masu naiman kasa Kasar Biafra, na karkashin kulawar gwamnatin tarayya inda ke fuskantar Shari’a.