Skip to content

Yawan samun hatsarurruka a wajen hakar ma’adanai

Cibiyar kula da hakan ma’adanai ta ƙasa ta koka bisa yadda ake samun yawan hatsarurka a wajajen hakan ma’adanai a Najeriya. Hakan ya biyo bayan ruftawar wani wajen hakan ma’adanai a ƙauyen Jagaba da ke ƙaramar hukumar Maru da ke cikin jiha Zamfara, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane goma sha uku 13 da kuma jikkata Wasu da dama.

A wata sanarwar haɗin gwiwa da suka sanyawa hannu shugabannin cibiyar, Temitope Olaipa da kuma Alhaji Abubakar Wushishi sun kwatanta wannan hadari a matsayin mai muni wanda kuma sakaci a ɓangaren da ke kula da ma’adanai ke haifar da shi.

Gwamnatin tarayya ta hannun ma’aikatar ma’adanai ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda gwamnati ta ce ta aike da wasu kwararru daga ma’aikatar ma’adanai zuwa jihar Zamfara domin kai ceton gaggawa, a cewa ma’aikatar ma’adanai wanann bala’in ya auku ne sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da akai ya sheƙawa, da kuma aikin masu hakan ma’adanai ba bisa ƙai’da ba.


Sai dai gwamnatin tarayya tuni ta aike da saƙon ta’aziyarta ga iyalan wadanda suka rasa rayukan su.