
Za a gina sansanin yiwa kasa hidima a Adamawa
Gwamnatin Jihar Adamawa ta sanar da shirin gina sansanin matasa masu yi wa kasa hidima na didindin a Makohi, da ke karamar hukumar Yola ta Kudu, a kan kuɗi naira biliyan 7.7
Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri, ya ce manufar aikin shi ne samar da muhalli kyau na zamani ga ‘yan masu yi wa kasa hidimar domin inganta rayuwarsu da ƙwarewarsu yayin aikin a jihar.
A wani ɓangare kuma, gwamnatin ta amince da kashe sama da naira biliyan 2 domin aikin gyarawa, sabuntawa, da sake fasalin asibitocin Cottage da ke Guyuk da Gulak a mataki na biyu.
Wannan shiri yana daga cikin ƙoƙarin gwamnatin Fintiri na ci gaba da ƙarfafa harkar lafiya da kuma inganta samun kulawar likitanci mai inganci a fadin Jihar Adamawa.

